Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Malaki 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Na ƙi Isuwa da zuriyarsa, na hallaka ƙasarsa ta kan tudu, wurin zamansa kuwa na ba namomin jeji.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 amma na ƙi Isuwa, na kuma mai da ƙasarsa da take kan duwatsu kango, na ba da gādonsa ga dilolin hamada.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Malaki 1:3
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Saboda kama-karyar da ka yi wa Yakubu ɗan'uwanka, Za a sa ka ka sha kunya, Za a hallaka ka har abada.


“Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,


Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka!


“Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi.


Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa.


Amma na tsiraita Isuwa sarai, Na buɗe wuraren ɓuyarsa, Har bai iya ɓoye kansa ba, An hallakar da mutanen Isuwa Tare da 'yan'uwansa da maƙwabtansa, Ba wanda ya ragu.


“Ni Ubangiji na ce, zan mai da Urushalima tsibin kufai, Wurin zaman diloli, Zan kuma mai da biranen Yahuza kufai, inda ba kowa.”


Yashi mai ƙuna kuma zai zama tafki, Ƙeƙasasshiyar ƙasa kuma za ta cika da maɓuɓɓugai. Inda diloli suka yi zama, Ciyawar fadama da iwa za su tsiro.


“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”


Ku mazaunan Dedan, ku juya, ku gudu, Ku ɓuya cikin zurfafa, Gama zan kawo masifa a kan Isuwa A lokacin da zan hukunta shi,


Domin haka, ku ji shirin da ni Ubangiji na yi wa Edom, da abin da nake nufin yi wa mazaunan Teman. Hakika za a tafi da su, har da ƙanana na garken tumaki, zan kuma sa wurin kiwonsu ya zama ƙeƙuwa saboda su.


Hazor za ta zama kufai har abada, wurin zaman diloli, Ba wanda zai zauna a ciki, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a wurin.”


Ya Sihiyona, hukunci a kan muguntarki ya ƙare, Ba zai ƙara barinki a ƙasar bauta ba. Amma zai hukunta ki saboda muguntarki, ya Edom, Zai tone zunubanki.


Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa a kan Edom, “Ba hikima kuma a cikin Teman? Shawara ta lalace a wurin masu basira? Hikima ta lalace ne?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ