A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.
“Kai Irmiya, sa'ad da wani mutum daga cikin mutanen nan, ko annabi, ko firist ya tambaye ka cewa, ‘Mece ce nawayar Ubangiji?’ Sai ka ce masa, ‘Ku ne nawayar, zan kuwa rabu da ku,’ ni Ubangiji na faɗa.
Mutanen Yahuza sun keta alkawarin da yake tsakaninsu da Allah, sun aikata mugun abu a Isra'ila, da a Urushalima. Gama sun ƙazantar da Haikalin da Ubangiji yake ƙauna, sun kuma auro matan da suke bauta wa gumaka.