to, takobin nan da kuke jin tsoro, zai ci muku can a ƙasar Masar, yunwan nan kuma da kuke jin tsoro za ta bi ku zuwa Masar ta tsananta muku, a can za ku mutu.
kuna cewa, ‘Mun ƙi, mu, ƙasar Masar za mu tafi, inda ba za mu ga yaƙi ba, ba za mu ji ƙarar ƙahon yaƙi ba, yunwa kuma ba za ta same mu ba, a can za mu zauna.’
Sa'an nan ya ce, “Ya Ubangiji, ka tsare ni daga shan jinin mutanen da suka sadaukar da ransu.” Saboda haka bai sha ruwan ba. Abubuwan da jarumawan nan uku suka yi ke nan.
Mala'ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa.