Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 5:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su, Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 5:7
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa, “ ‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masu tsami, Haƙoran 'ya'ya suka mutu’ ba.


Ku kuma kun yi laifi fiye da na kakanninku. Kowannenku kuwa ya bi tattauran mugun nufin zuciyarsa, yana ƙin kasa kunne gare ni.


“Me kuke nufi da faɗar wannan karin magana a kan ƙasar Isra'ila cewa, “ ‘Ubanni sun ci 'ya'yan inabi masu tsami, Hakoran 'ya'ya kuwa sun mutu’?


Mun san muguntar da muka yi, ya Ubangiji, Da wadda kakanninmu suka yi, Gama mun yi maka zunubi.


Kada ka rusuna musu, kada kuwa ka bauta musu, gama ni Ubangiji Allahnka, mai kishi ne. Nakan hukunta 'ya'ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina.


Ga abin da Ubangiji ya ce, “An ji murya daga Rama, Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta, ba su.


Sai Yakubu mahaifinsu, ya ce musu, “Kun sa ni rashi, ga shi, ba Yusufu, Saminu ba shi, wai kuma yanzu za ku ɗauki Biliyaminu, ga dai irin abubuwan da suka faɗo mini.”


To, ina kakannin nan naku suke? Annabawan fa? Suna da rai har wa yau?


Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”


Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba. Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan.


Suka ce, “Mu bayinka, 'yan'uwan juna ne, mu goma sha biyu muke maza, 'ya'yan mutum guda a ƙasar Kan'ana, ga shi kuwa autanmu yana tare da mahaifinmu a yanzu, ɗayan kuwa ya rasu.”


‘Ubangiji mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, kana gafarta mugunta da laifi, amma ba za ka ƙyale mai laifi ba, gama kakan ɗora wa 'ya'ya alhakin muguntar iyaye, har tsara ta uku da ta huɗu.’


Sai ka faɗa musu cewa, Ubangiji ya ce, ‘Domin kakanninku sun rabu da ni, sun bi gumaka, sun bauta musu, sun yi musu sujada. Sun rabu da ni, sun ƙi kiyaye dokokina.


Kina ɗauke da hukuncin lalatarki da na abubuwanki masu banƙyama, ni Ubangiji na faɗa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ