“Ubangiji ya tattara laifofina Ya yi karkiya da su, Ya ɗaura su a wuyana, Ya sa ƙarfina ya kāsa. Ya kuma bashe ni a hannun Waɗanda ban iya kome da su ba.
Gama haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, na faɗa. Na sa wa wuyan dukan waɗannan al'ummai karkiya ta ƙarfe, don su bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila, za su kuwa bauta masa, gama na ba shi su, har da namomin jeji.’ ”
“ ‘Amma idan wata al'umma ko wani mulki bai yarda ya bauta wa Nebukadnezzar, Sarkin Babila ba, bai kuma ɗaura karkiyar Sarkin Babila a wuyansa ba, zan hukunta wa wannan al'umma da takobi, da yunwa, da annoba, har in hallaka ta, ta hannun Nebukadnezzar, ni Ubangiji na faɗa.
domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.
“Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, Za a baje garun nan na Babila mai fāɗi Za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta. Mutane sun wahalar da kansu a banza. Sauran al'umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”
Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.
Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.