Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba!
Ƙaƙa ka zama kamar wanda bai san abin da zai yi ba, Kamar jarumin da ya kasa yin ceto? Duk da haka, ya Ubangiji, kana nan a tsakiyarmu. Da sunanka ake kiranmu, Kada ka bar mu!”