Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 5:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Rawani ya fāɗi daga kanmu, Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 5:16
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka, Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.


Gama ya kwashe dukiyata duka, Ya ɓata mini suna.


Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!


Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.


Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.


Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne, Da muguntar firistoci, Waɗanda suka kashe adalai.


Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa! Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa. Bai kuma tuna da matashin sawayensa ba A ranar fushinsa.


“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!


Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske, Saboda haka ta ƙazantu, Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina ta Domin sun ga tsiraicinta, Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.


“Al'amuranki da ayyukanki suka jawo miki wannan halaka, Tana da ɗaci kuwa, Ta soki har can cikin zuciyarki.”


Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.”


Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kanka wannan, Da ka rabu da Ubangiji Allahnka, Sa'ad da ya bishe ka a hanya.


Adalci yakan ɗaukaka al'umma, amma zunubi yakan kunyatar da al'umma.


Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


domin dukiya ba ta tabbata har abada, al'ummai ma haka ne.


Isra'ilawa fa suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa, suka zuba a gaban Ubangiji. Suka yi azumi a ranan nan, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi.” Sama'ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra'ilawa.


Hakika Urushalima ta shiga uku! Yahuza tana kan fāɗuwa! Duk abin da suke faɗa, da abin da suke yi, na gāba da Ubangiji ne, a fili suke raina Allah, shi kansa.


Amma sa'ad da suka shiga cikinta suka mallake ta, ba su yi biyayya da muryarka ba, ba su kiyaye dokokinka ba, ba su aikata dukan abin da ka umarce su ba, saboda haka ka sa wannan masifa ta auko musu.


“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.


Domin haka zan buge ku da ciwo, In maishe ku kufai saboda zunubanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ