Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Gara ma waɗanda takobi ya kashe Da waɗanda yunwa ta kashe, Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Gara waɗanda aka kashe su da takobi da waɗanda suke mutuwa da yunwa; sun rame domin rashin abinci a gona.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 4:9
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ku naɗa rawunanku, ku sa takalmanku, ba za ku kuma yi makoki ko kuka ba, amma za ku lalace cikin zunubanku. Za ku yi ta nishi.


Sauranku da kuka ragu za ku lalace a ƙasashen maƙiyanku saboda muguntarku da ta kakanninku, za ku lalace kamarsu.


“Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’


za su mutu da muguwar cuta. Ba za a yi makoki dominsu ba, ba kuwa za a binne su ba. Za su zama juji. Takobi da yunwa za su kashe su, gawawwakinsu za su zama abincin tsuntsayen sararin sama da na namomin jeji.”


“Da ma mun mutu ta ikon Ubangiji a ƙasar Masar lokacin da muka zauna kusa da tukwanen nama, muka ci abinci muka ƙoshi. Ga shi, kun fito da mu zuwa cikin jeji don ku kashe dukan wannan taro da yunwa.”


A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar.


Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.


Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali. Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.


Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ga shi, zan datse abinci a Urushalima. Za su auna abincin da za su ci da tsoro, su kuma auna ruwan da za su sha da damuwa.


Takobi yana zare a waje, annoba da yunwa suna ciki. Wanda yake waje takobi zai kashe shi, wanda kuma yake ciki annoba da yunwa za su kashe shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ