8 Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako, Ya yi watsi da addu'ata.
8 Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
Da rana na yi kira a gare ka, ya Allahna, Amma ba ka amsa ba. Da dare kuma na yi kira, Duk da haka ban sami hutawa ba.
“Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba, Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.
Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba, Amma ba wanda ya kasa kunne. Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.
Wajen ƙarfe uku kuma sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktāni?” Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”
Ya Ubangiji, ina ta kukan neman taimako, Amma ka ƙi ji, sai yaushe za ka ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci, Amma ba ka yi taimako ba.
Ka kuma rufe kanka da gajimare Don kada addu'a ta kai wurinka.
Har yaushe ke nan ya Ubangiji Allah Mai Runduna, Za ka yi ta fushi da addu'o'in jama'arka?
“Ka yafa fushi, ka runtume mu, Kana karkashe mu ba tausayi.
Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.