sai ka yi annabci ka ce, ni Ubangiji Allah na ce, ‘Da yake sun maishe ku kufai marar amfani, sun kuma murƙushe ku ta kowace fuska, har kun zama abin mallakar sauran al'umma, kun zama abin magana da abin tsegumi ga mutane.
Sa'an nan suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya, gama firist ba zai bar bin shari'a ba. Haka nan ma masu hikima ba za su bar yin shawara ba, haka nan kuma annabi ba zai bar yin magana ba! Ku zo mu kai ƙararsa, kada mu kula da abin da zai faɗa.”