Da ba domin Allah na mahaifina da Ibrahim, da martabar Ishaku na wajena ba, hakika da yanzu ka sallame ni hannu wofi. Allah ya ga wahalata da aikin hannuwana, ya kuwa tsauta maka a daren jiya.”
Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina.
Amma kana gani, kana kuma lura da masu shan wuya, da masu ɓacin rai, Koyaushe kuma a shirye kake ka yi taimako. Mutum wanda ba shi da mai taimako yakan danka kansa gare ka, Gama kullum kakan taimaki masu bukata.