Mai fansarsu mai ƙarfi ne, Ubangiji Mai Runduna ne sunansa. Hakika zai tsaya musu don ya kawo wa duniya salama, Amma zai kawo wa mazaunan Babila fitina.
Mala'ikan da ya fanshe ni Daga dukan mugunta, Ya sa wa samarin albarka, Bari a dinga ambatarsu da sunana, Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena, Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama taron jama'a a tsakiyar duniya.”
Sa'ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.” Sa'an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.
Amma ya Ubangiji Mai Runduna, mai shari'ar adalci, Kakan gwada zuciya da tunani, Ka yarda mini in ga sakayyar da za ka yi mini a kansu, Gama a gare ka na danƙa maganata.