Ya Ubangiji, ka dube mu daga Sama, wurin da kake cike da tsarki da ɗaukaka. Ina kulawan nan da kake yi mana? Ina ikon nan naka? Ina ƙaunan nan taka da juyayin nan naka? Kada ka watsar da mu.
Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?