4 Ya sa naman jikina da fatar jikina su lalace, Ya kuma kakkarya ƙasusuwana.
4 Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.
Dare farai na yi ta kuka saboda azaba, Sai ka ce zaki yake kakkarya ƙasusuwana. Na zaci Allah zai kashe ni.
Bari in ji sowa ta farin ciki da murna. Ko da yake ka ragargaza ni, Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.
Sa'ad da ban hurta zunubaina ba, Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.
Ƙarfina ya ƙare, Ya rabu da ni kamar ruwan da ya zube ƙasa. Dukan gaɓoɓina sun guggulle, Zuciyata ta narke kamar narkakken kakin zuma.
Fatata ta takura, ta zama baƙa, Ƙasusuwana suna zogi saboda zafi,