Gama haka Ubangiji ya faɗa, “Daidai kamar yadda na kawo wannan babbar masifa a kan jama'an nan, haka kuma zan kawo musu dukan waɗannan alherai da na alkawarta musu.
Ayuba ya amsa, ya ce mata, “Wace irin maganar gāɓanci ce haka? Lokacin da Allah ya aiko mana da alheri, mukan yi na'am da shi, to, me zai sa sa'ad da ya aiko mana da wahala za mu yi gunaguni?” Cikin dukan wahalar da Ayuba ya sha, bai sa wa Allah laifi ba.