“Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,
Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari'ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu.