Idan a iya auna sammai a kuma iya bincike tushen duniya a ƙarƙas, To, ashe, zan watsar da dukan zuriyar Isra'ila ke nan saboda dukan abin da suka yi, Ni Ubangiji na faɗa.
Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.