Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 3:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 3:26
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.


Ka sa zuciyarka ga Ubangiji Ka kiyaye dokokinsa, Shi zai ba ka ƙarfin da za ka mallaki ƙasar, Za ka kuwa ga an kori mugaye.


Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji, Ga maganarsa na dogara.


Saboda haka, kada ku yar da amincewar nan taku, domin tana da sakamako mai yawa.


Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.


Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddin muna tsaye da ƙarfi a kan amincewar nan tamu ta fari, har zuwa ƙarshe.


Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!


Ina jiranka ka cece ni, ya Ubangiji, Ina aikata abin da ka umarta.


Ina sa zuciya ga cetonka ƙwarai, ya Ubangiji! Ina samun farin ciki ga dokarka.


Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”


Da murna zan miƙa maka hadaya, Zan yi maka godiya, ya Ubangiji, Domin kai mai alheri ne.


Zan gode maka, ya Ubangiji, Saboda abin da ka aikata. Zan dogara gare ka, Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka, Domin kai mai alheri ne.


Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah! Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah, Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.


Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.


Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”


Abu mai kyau ne a yi wa Ubangiji godiya, A raira waƙa don girmansa, Allah mafi ɗaukaka,


Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.


Faɗa masa ya zauna da shiri, ya natsu, kada ya ji tsoro ko ya damu. Fushin sarki Rezin da Suriyawansa da na sarki Feka ba wani abu mai hatsari ba ne, bai fi hayaƙin 'yan ƙirare biyu da suke cin wuta ba.


A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”


Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.


Ubangiji zai yi yaƙi dominku, sai dai ku tsaya kurum!”


Shi kaɗai ne mai kiyaye ni, Mai Cetona, Shi ne kariyata, Ba kuwa za a yi nasara da ni ba sam.


Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ