Makoki 3:19 - Littafi Mai Tsarki19 Ka tuna da azabata, da galabaitata, Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ya Allah, Allahnmu, da girma kake! Kai mai banrazana ne, cike da iko! Da aminci ka cika alkawaranka da ka alkawarta. Daga lokacin da Sarkin Assuriya ya danne mu, Har yanzu ma, wace wahala ce ba mu sha ba! Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu, Da annabawanmu, da kakanninmu, Da dukan sauran jama'arka sun sha wahala. Ka san irin wahalar da muka sha.