Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 3:17 - Littafi Mai Tsarki

17 An raba ni da salama, Na manta da abar da ake ce da ita wadata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 3:17
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dukanmu muna gurnani kamar beyar, muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci, amma ina. Muna ta neman ceto, amma ya yi nisa da mu.


Gama kafin waɗannan kwanaki, mutum da dabba ba su da abin yi. Ba kuma zaman lafiya ga mai fita da shiga saboda maƙiya, gama na sa kowane mutum ya ƙi ɗan'uwansa.


“Ina kuka saboda waɗannan abubuwa, Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna. Gama mai ta'azantar da ni, Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni. 'Ya'yana sun lalace, Gama maƙiyi ya yi nasara!”


Ubangiji kuma ya ce, “Kada ka shiga gidan da ake makoki, ko ka tafi inda ake baƙin ciki, kada ka yi baƙin ciki saboda su, gama na ɗauke salamata, da ƙaunata, da jinƙaina daga wurin jama'an nan.


“Ka ƙi Yahuza ke nan ɗungum? Ranka kuma yana jin ƙyamar Sihiyona ne? Me ya sa ka buge mu, har da ba za mu iya warkewa ba? Mun zuba ido ga samun salama, amma ba wani abin alheri da ya zo. Mun kuma sa zuciya ga warkewa, amma sai ga razana.


Mun sa zuciya ga salama, amma ba lafiya, Mun sa zuciya ga lokacin samun warkewa, Amma sai ga razana!


Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.


Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama. Ka ceci raina daga dukan hatsari, Ka gafarta dukan zunubaina.


Ba za a ceci mugaye ba, Saboda ba su yi biyayya da dokokinka ba.


“Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai, Farin cikina ya riga ya ƙare.


amma a bayansu za a yi shekara bakwai na yunwa, amma za a manta da dukan ƙoshin nan a ƙasar Masar, yunwar kuwa za ta game dukan ƙasar.


A kan dukan tsaunukan nan na hamada Masu hallakarwa sun zo, Gama takobin Ubangiji yana ta kisa Daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, Ba mahalukin da yake da salama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ