13 Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa.
13 Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau, Dafinsu kuwa ya ratsa jikina. Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.
Kibiya ba za ta sa ya gudu ba, Jifar majajjawa a gare shi kamar jifa da tushiyoyi ce.
“ ‘Zan tula musu masifu, Zan ƙare kibauna a kansu,
Kwarinsu kamar buɗaɗɗen kabari ne, Dukansu jarumawa ne.
Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.