Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Makoki 2:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Ya Ubangiji, ka duba, ka gani! Wane ne ka yi wa haka? Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno? Ko kuwa za a kashe firist da annabi A cikin Haikalin Ubangiji?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 “Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Makoki 2:20
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mata masu juyayi, da hannuwansu Suka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa, Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.


Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’


Aka karkashe firistoci da takuba, Matansu ba su yi makoki dominsu ba.


Dalili kuwa saboda zunuban annabawa ne, Da muguntar firistoci, Waɗanda suka kashe adalai.


Na roƙi Ubangiji, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah, kada ka hallaka jama'arka, abar gādonka wadda ka fanshe ta ta wurin girmanka, waɗanda kuma ka fito da su daga Masar da ikon dantsenka.


Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?


Ubanni za su cinye 'ya'yansu, 'ya'ya kuma za su cinye ubanninsu. Zan hukunta ki, waɗanda kuma suka tsira zan watsar da su ko'ina.


Ubangiji kansa ya watsar da su, Ba zai ƙara kulawa da su ba. Ba su darajanta firistoci ba, Ba su kuma kula da dattawa ba.


“Na kira masoyana, amma suka yaudare ni, Firistocina da dattawana a cikin birni sun hallaka Saboda neman abincin da za su ci su rayu.


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Za ku ci naman 'ya'yanku mata da na 'ya'yanku maza.


Birnin duka ya ruguntsume, cike da hayaniya da tashin hankali. Mutanenku da suka mutu ba su mutu suna yaƙi ba.


Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’


Ya kuma ce musu, “Ku ƙazantar da Haikalin, ku cika farfajiya da kisassu, sa'an nan ku tafi!” Sai suka tafi, suka yi ta kashe mutanen da suke cikin birnin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ