Makoki 2:2 - Littafi Mai Tsarki2 Dukan wuraren zaman Yakubu, Ubangiji ya hallakar ba tausayi, Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Ubangiji ya hallakar da wurin zaman Yaƙub ba tausayi; A cikin fushinsa kuma zai rurrushe kagaran Diyar Yahuda. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan wannan zan ceci Zadakiya Sarkin Yahuza, shi da bayinsa, da mutanen birnin nan waɗanda suka tsira daga annoba, da takobi, da yunwa, zan bashe su a hannun Nebukadnezzar Sarkin Babila, da hannun abokan gābansu, da waɗanda suke neman rayukansu. Zai kashe su da takobi, ba zai ji tausayinsu, ko ya rage waɗansunsu, ko ya ji juyayinsu ba.’
Ubangiji ya tambaye shi, ya ce, “Ko ka lura da bawana Ayuba? Ba wani mutumin kirki, mai aminci, kamarsa a duniya. Yana yi mini sujada, natsattse ne, yana ƙin aikata kowace irin mugunta. Kai ka sa na yardar maka ka far masa, ba tare da wani dalili ba. Amma duk da haka Ayuba yana nan da amincinsa kamar yadda yake.”