Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 9:57 - Littafi Mai Tsarki

57 Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba'al, kuma ya kama su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

57 Allah kuma ya sa muguntar mutanen Shekem suka koma kansu. La’anar Yotam ɗan Yerub-Ba’al kuma ta kama su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 9:57
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma idan ba haka yake ba, Allah ya sa wuta ta fito daga wurin Abimelek ta cinye mutanen Shekem da na Bet-millo. Bari Allah ya sa kuma wuta ta fito daga wurin mutanen Shekem da na Bet-millo ta cinye Abimelek.”


A cikin kwanakinsa, Hiyel mutumin Betel ya gina Yariko. Ya yi hasarar ɗan farinsa, Abiram, sa'ad da ya kafa harsashin ginin, ya kuma yi hasarar autansa, Segub, sa'ad da ya sa ƙofofin, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Joshuwa ɗan Nun.


Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.


A lokacin nan Joshuwa ya yi musu magana da rantsuwa ya ce, “La'ananne ne mutum a gaban Ubangiji Wanda ya tashi don ya sāke gina birnin nan Yariko. A bakin ɗan farinsa zai kafa tushensa, A bakin autansa kuma zai gina ƙofofinsa.”


Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa.


Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe 'yan'uwansa maza, su saba'in.


Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu.


Ubangiji zai ɗora masa alhakin mugayen ayyukansa, gama ya kashe mutum biyu ba da sanin tsohona Dawuda ba, waɗanda kuma suka fi shi adalci, wato Abner ɗan Ner, shugaban sojojin Isra'ila, da Amasa ɗan Yeter, shugaban sojojin Yahuza.


Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.


Yau na raunana, ko da yake ni sarki ne naɗaɗɗe. Waɗannan mutane, 'ya'yan Zeruya, sun fi ƙarfina, Ubangiji ya sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata.”


Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa, Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.


Shi zai hukunta su saboda muguntarsu, Ya hallaka su saboda zunubansu. Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.


Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.


Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ