47 Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya.
47 Da Abimelek ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru a can,
Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira.
Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi.