42 Kashegari mutanen Shekem suka tafi saura, sai aka faɗa wa Abimelek.
42 Kashegari mutanen Shekem suka tafi gonaki, aka kuwa gaya wa Abimelek.
Sai Abimelek ya zauna a Aruma. Zebul kuwa ya kori Ga'al da 'yan'uwansa, ya hana su zama a Shekem.
Shi ma ya kwashi mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, suka yi kwanto a saura. Da ya duba, ya ga mutane suna fitowa daga cikin birnin. Ya fāɗa musu, ya karkashe su.