39 Ga'al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek.
39 Saboda haka Ga’al ya fito da ’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek.
Sa'an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?’ Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.”
Abimelek kuwa ya runtumi Ga'al, shi kuwa ya gudu. Mutane da yawa suka ji rauni, ya bi su har bakin ƙofar birnin.