22 Abimelek kuwa ya yi shekara uku, yana mulkin Isra'ila.
22 Bayan Abimelek ya yi shekara uku yana mulki a Isra’ila,
Sa'an nan Yotam ya tsere. Ya tafi ya zauna a Biyer, gama yana tsoron ɗan'uwansa Abimelek.
Ubangiji kuma ya sa husuma ta tashi tsakanin Abimelek da mutanen Shekem. Shugabannin Shekem kuwa suka tayar masa.
Shekara ɗari uku Isra'ilawa suka yi zamansu a Heshbon da ƙauyukanta, da Arower da ƙauyukanta, da dukan biranen da suke a gefen Kogin Arnon, me ya sa ba ka ƙwace su tun a wancan lokaci ba?