Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 8:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Shugabannin Sukkot kuwa suka ce, “Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka abinci?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 8:6
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarki Ahab ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, sojan ainihi, sai ya gama yaƙi sa'an nan ya yi fāriya, amma ba tun kafin a fara ba.”


Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.


Matalauci yakan yi roƙo da taushi, maganar matalauci rarrashi ne, amma attajiri yakan yi magana garas.


Yehowash Sarkin Isra'ila ya mayar wa Amaziya Sarkin Yahuza da amsa cewa, “A dutsen Lebanon ƙaya ta aika wurin itacen al'ul ta ce, ‘Ka ba ɗana 'yarka ya aura.’ Sai mugun naman jeji na Lebanon ya wuce, ya tattake ƙayar.


Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”


Mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ka la'anta Meroz, Ka la'anta mazauna cikinta sosai, Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba, Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”


Da Madayanawa, fatake, suna wucewa, sai suka jawo Yusufu suka fitar da shi daga cikin rijiyar suka sayar wa Isma'ilawa a bakin azurfa ashirin, aka kuwa tafi da Yusufu zuwa Masar.


Suka zauna su ci abinci, da suka ɗaga ido suka duba, sai ga ayarin Isma'ilawa suna zuwa daga Gileyad, da raƙumansu ɗauke da ƙāro, da man ƙanshi na wartsakewa, da mur, suna gangarawa kan hanyarsu zuwa Masar.


Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Isma'ilu, maza, bisa ga haihuwarsu. Nebayot ɗan farin Isma'ilu, da Kedar, da Adbeyel, da Mibsam,


Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ