Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 8:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Gidiyon ya ce wa mutanen Sukkot, “Ina roƙonku, ku ba mutanen da suke tare da ni abinci, gama sun gaji, ga shi kuwa, ina runtumar Zeba da Zalmunna, sarakunan Madayanawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 8:5
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yakubu ya kama hanya zuwa Sukkot, ya kuwa gina wa kansa gida, ya yi wa shanunsa garke. Saboda haka aka sa wa wurin suna Sukkot.


A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce, “Da nasara zan raba Shekem, Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.


Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.


domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku.


Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.


Zeba da Zalmunna kuwa suna Karkor tare da rundunarsu, mutum wajen dubu goma sha biyar (15,000), waɗanda suka ragu daga cikin rundunar mutanen gabas, gama an kashe mutum dubu ɗari da dubu ashirin (120,000), masu takuba.


Zeba da Zalmunna, sarakunan nan biyu na Madayana suka gudu, amma ya bi su, ya kamo su. Ya sa dukan rundunarsu ta gigice.


Sa'an nan ya zo wurin mutanen Sukkot ya ce musu, “To, ga Zeba da Zalmunna waɗanda kuka yi mini ba'a saboda su, kuna cewa, ‘Ba ka riga ka kama Zeba da Zalmunna ba, ta yaya za mu ba sojojinka da suka gaji abinci?’ To, ga su!”


Mala'ikan Ubangiji ya ce, “Ka la'anta Meroz, Ka la'anta mazauna cikinta sosai, Gama ba su kawo wa Ubangiji gudunmawa ba, Su zo su yi yaƙi kamar sojoji dominsa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ