Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe 'yan'uwansa maza, wato 'ya'yan Yerubba'al, mutum saba'in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba'al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya.
“Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, ‘Me ya fi muku kyau, 'ya'yan Yerubba'al, maza saba'in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?’ Amma ku tuna fa ni jininku ne.”
Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.
Ahab yana da 'ya'ya maza saba'in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da 'ya'yan Ahab.
Yana da 'ya'ya maza talatin, da 'ya'ya mata talatin. Ya aurar da 'ya'yansa mata ga wata kabila, ya kuma auro wa 'ya'yansa maza 'yan mata daga wata kabila. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara bakwai.
Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.
Amma ga shi, yau kun juya kuna gāba da gidan mahaifina. Kun kashe 'ya'yansa maza, su saba'in, a dutse guda, kuka naɗa Abimelek, ɗan da baiwa ta haifa, ya zama sarki a Shekem, don dai kawai shi ɗan'uwanku ne.