Sai Yerubba'al, wato Gidiyon, da mutanen da suke tare da shi suka yi sammako, suka kafa sansaninsu kusa da maɓuɓɓugan Harod. Madayanawa kuwa suka kafa sansaninsu a arewa da su, kusa da tudun More a kwarin.
Ubangiji kuwa ya aika musu da Yerubba'al, wato Gidiyon, da Barak, da Yefta, da Samson, suka cece ku daga hannun abokan gābanku ta kowace fuska. Sa'an nan kuka yi zamanku lafiya.