Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 8:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Nauyin 'yan kunnen zinariya da ya roƙa ya kai shekel dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), banda kayan ado, da na rataye-rataye, da tufafin shunayya waɗanda sarakunan Madayanawa suke sawa, banda ɗan gaba da yake a wuyan raƙumansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Nauyin ’yan kunnen zinariyar ya kai shekel ɗari goma sha bakwai, ban da kayan ado, abin wuya da tufafin shunayya waɗanda sarakuna Midiyawa suke sawa ko sarƙoƙin da suke wuyar raƙumansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 8:26
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Kaito! Kaiton babban birnin nan! Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini, Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u!


wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi,


Sa'an nan Yesu ya fito, sāye da kambin ƙayar, da alkyabba mai ruwan jar garura. Sai Bilatus ya ce musu, “To, ga mutumin!”


Sai soja suka yi wani kambi na ƙaya suka sa masa a kā, suka yafa masa wata alkyabba mai ruwan jar garura.


An kawo fallayen azurfa daga Tarshish, Da zinariya kuma daga Ufaz, Aikin gwanaye da maƙeran zinariya. Tufafinsu na mulufi ne da shunayya, duka aikin gwanaye.


Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu launin shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai launin shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shushan.


Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.


An yi filafilan jirgin ruwanki da lilin mai kyau, mai ado daga Masar, Don ya zama alama. An yi tutar jirgin ruwanki da shuɗi da shunayya na gaɓar tekun Elisha.


“An yi wani mai arziki, mai sa tufafin jan alharini da farare masu ƙawa, yana shan daularsa a kowace rana.


Sai Zeba da Zalmunna suka ce, “Tashi da kanka, ka kashe mu, gama yadda mutum yake haka kuma ƙarfinsa yake.” Gidiyon kuwa ya tashi ya kashe Zeba da Zalmunna. Ya kwance kayan ado daga wuyan raƙumansu.


Suka ce, “Lalle, za mu ba ka su.” Nan da nan suka shimfiɗa mayafi, kowa ya zuba 'yan kunnen da ya kwaso ganima.


Gidiyon kuwa ya yi gunki da zinariyar, ya ajiye a birninsa, wato Ofra. Isra'ilawa kuma suka bar bin Allah, suka tafi can domin su yi wa gunkin sujada, ya zama tarko ga Gidiyon da iyalinsa.


Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa, tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.


Rana tana zuwa sa'ad da Ubangiji zai raba matan Urushalima da dukan abin da suke taƙama da shi, da kayan adon da suke sawa a ƙafafunsu, da kawunansu, da wuyansu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ