Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 7:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Kowannensu ya yi tsaye a inda yake kewaye da sansanin. Dukan rundunar Madayanawa kuwa suka gudu, suna ihu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Yayinda kowannensu ya tsaya a inda yake kewaye da sansanin, dukan Midiyawa suka fito da gudu, suna kuka yayinda suke gudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 7:21
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mugun mutum yakan gudu, alhali kuwa ba mai korarsa, amma amintaccen mutum kamar zaki yake, ba shi da tsoro.


Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya ce wa jama'a, “Ku komo gare ni a natse, ku dogara gare ni. Sa'an nan za ku zama ƙarfafa ku zauna lafiya.” Amma ba ku yarda ba!


Taimakon da Masar za ta yi marar amfani ne. Don haka na yi mata laƙabi, ‘Macijin da ba ya yin kome.’ ”


Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”


Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”


suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.


Ƙungiyoyi uku ɗin nan suka busa ƙahonin, suka fasa tuluna. Suka riƙe jiniyoyi a cikin hannuwansu na hagu, da ƙahonin busawa a hannuwansu na dama. Sai suka yi kuwa, suka ce, “Takobin Ubangiji da na Gidiyon!”


kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.


Sai Yahaziyel ya ce, “Ku ji, ku dukanku, mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima, da sarki Yehoshafat, ga abin da Ubangiji yake faɗa muku, ‘Kada ku ji tsoro, ko ku razana saboda wannan babban taro, gama wannan yaƙi ba naku ba ne, amma na Allah ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ