Mahukunta 7:14 - Littafi Mai Tsarki14 Abokinsa ya amsa, ya ce, “Ai, ba wani abu ba ne. Wannan takobin Gidiyon ne, ɗan Yowash. Ba'isra'ile! Allah ya ba shi nasara kan Madayanawa da dukan rundunanmu!” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da dukan sarakunan Amoriyawa waɗanda suke wannan hayi, wato yamma da Urdun, da dukan sarakunan Kan'aniyawa da suke bakin teku, suka ji yadda Ubangiji ya sa ruwan Urdun ya ƙafe don Isra'ilawa, har suka haye, sai zukatansu suka narke, har ba wanda yake da sauran kurwa a cikinsu saboda tsoron Isra'ilawa.