Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 6:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Ya aika manzanni ko’ina a Manasse, yana kiransu su kintsa, haka ma Asher, Zebulun da Naftali, ta haka su ma suka haura su sadu da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 6:35
6 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ta aika a kirawo Barak, ɗan Abinowam, daga birnin Kedesh a ƙasar Naftali. Ta ce masa, “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ba ka wannan umarni, ya ce, ‘Ka tafi ka tara mutanenka a Dutsen Tabor, ka kuma ɗauki mutum dubu goma (10,000), daga kabilar Naftali da ta Zabaluna.


Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi.


Amma mutanen Zabaluna da na Naftali Suka kasai da ransu a bakin dāga.


Yanzu sai ka ce wa mutanen, ‘Duk mai jin tsoro da mai rawar jiki, ya koma gida!’ ” Da Gidiyon ya gwada su, mutum dubu ashirin da biyu (22,000) suka koma, dubu goma (10,000) suka tsaya.


Jama'ar kabilar Naftali, da Ashiru, da Manassa, suka ji kira, suka fito, suka runtumi Madayanawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ