Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 6:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Sa’an nan ka gina bagade irin da ya dace wa Ubangiji Allahnka a kan wannan tudu. Ka yi amfani da itacen katakon ginshiƙin Ashera da ka sare, ka miƙa bijiman nan biyu hadaya ta ƙonawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 6:26
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai dai a yi kome ta hanyar da ta dace, a shirye kuma.


domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne. Haka yake kuwa a duk ikilisyoyin tsarkaka.


A ran nan Gad ya koma wurin Dawuda ya ce masa, “Ka haura ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.”


Sai ku rurrushe bagadansu, ku farfashe al'amudansu, ku sassare gumakansu.


A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.


Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare.


Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji.


Arauna kuwa ya ce wa Dawuda, “Bari ubangijina, sarki, ya karɓa, ya yi abin da yake so. Ga shanun nan domin hadayar ƙonawa, ga kuma itacen sussuka da karkiya domin itacen hadayar.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ