Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 6:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Da kan sandan da yake a hannunsa, mala’ikan Ubangiji ya taɓa naman da burodi marar yistin. Sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da burodin. Mala’ikan kuwa ya ɓace.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 6:21
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji, ta ƙone hadaya ta ƙonawa da kitsen a bisa bagaden. Da jama'a duka suka gani, suka yi ihu, suka fāɗi rubda ciki suka yi sujada.


Sa'ad da Sulemanu ya gama yin addu'arsa, sai wuta ta sauko daga sama, ta cinye hadayar ƙonawa tare da sauran hadayu, darajar Ubangiji kuma ta cika Haikalin.


Ubangiji kuwa ya sa wuta ta faɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsun, da ƙurar, ta kuma lashe ruwan da yake cikin wuriyar.


Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai ya yi roƙo ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya amsa masa ta wurin wutar da ta sauko daga sama a bisa bagaden hadayar ta ƙonawa.


Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.


Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi.


Manowa kuwa ya yanka ɗan akuya, ya kuma kawo hadayar gāri, ya miƙa a kan dutse ga Ubangiji, mala'ika kuma ya yi al'ajabi. Manowa da matarsa suka yi kallo.


Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ubangiji zai nuna maka alama da za ta tabbatar maka zai cika alkawarinsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ