Mahukunta 6:13 - Littafi Mai Tsarki13 Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |