Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 5:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ku kasa kunne! Da hayaniya mutane a bakin rijiyoyi Suna ba da labarin nasarar Ubangiji, Wato nasarar jama'ar Isra'ila! Sa'an nan jama'ar Ubangiji Suna tahowa daga biranensu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 da muryoyin mawaƙa a wuraren ruwaye. Suna faɗi ayyukan adalcin Ubangiji, ayyukan adalcin mayaƙansa a Isra’ila. “Sa’an nan mutanen Ubangiji suka gangara zuwa ƙofofin birni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 5:11
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya ku jama'ata, ku tuna Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla, Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya amsa masa, Da abin da ya faru daga Shittim, har zuwa Gilgal, Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.”


Yanzu fa ku tsaya shiru don in yi muku magana a kan ayyuka masu adalci na Ubangiji waɗanda ya aikata dominku da kakanninku.


Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.


Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci, Domin akwai masu kisa a jeji.


Dole ne mu biya ruwan da za mu sha, Dole ne kuma mu sayi itace.


“Ka tafi ka tsaya a ƙofar Haikalin Ubangiji, ka yi shelar wannan magana, ka ce, su kasa kunne ga maganar Ubangiji, dukansu mutanen Yahuza, su da suke shiga ta ƙofofin nan don su yi wa Ubangiji sujada!


Zai ba da ruhun adalci ga waɗanda suke alƙalai, ƙarfin hali kuma ga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofin birni.


Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su.


A sa'ad da nakan tafi kofar birni, In shirya wurin zamana a dandali,


sai a kawo su, su biyu ɗin, a dandalin ƙofar gari, ku jajjefe su da duwatsu har su mutu, don yarinyar tana cikin gari, amma ba ta yi kururuwa a taimake ta ba, don kuma mutumin ya ɓata budurwar maƙwabcinsa. Da haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.


Za su ba da labarin girmanka duka, Su kuma raira waƙa a kan alherinka.


Ya durƙusar da raƙumansa a bayan birnin, kusa da bakin rijiyar ruwa da maraice, wato lokacin da mata sukan tafi ɗebo ruwa.


Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.


A sa'ad da garkunan suka tattaru a wurin, makiyayan sukan kawar da dutsen daga bakin rijiyar, su shayar da su, sa'an nan su mayar da dutsen a wurinsa, a bisa bakin rijiya.


Zai zaɓar wa kansa wuri mai kyau, Gama wurin ne aka keɓe wa shugaba. Ya zo wurin shugabannin mutane, Tare da Isra'ila, ya aikata adalcin Ubangiji, Ya kiyaye farillansa.”


wato matan Isra'ilawa sukan fita kowace shekara su yi makoki kwana huɗu don 'yar Yefta, mutumin Gileyad.


Zan ba da labarin adalcinka, Zan yi magana a kan cetonka duk yini, Ko da yake ya fi ƙarfin in san shi duka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ