Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.
Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka. Ka aikata al'amura masu banmamaki, Ka tafiyar da su da aminci, Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.
Sai kowane mutumin Yahuza da na Urushalima, tare da Yehoshafat shugabansu, suka koma Urushalima suna murna, gama Ubangiji ya sa su yi farin ciki saboda maƙiyansu.
Sa'ad da ya yi shawara da jama'a, sai ya zaɓi waɗanda za su raira waƙa ga Ubangiji, su yabe shi a natse sa'ad da suke tafe a gaban runduna, su ce, “Ku yi godiya ga Ubangiji, Saboda madawwamiyar ƙaunarsa Tabbatacciya ce har abada.”
Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce, “Ubangiji ya cika zuciyata da murna. Ina farin ciki da abin da ya yi. Ina yi wa maƙiyana dariya, Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.