Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Debora ta ce, “To, shi ke nan, zan tafi tare da kai. Amma saboda yadda ka ɗauki wannan batun, darajar ba za tă zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Saboda haka Debora ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 4:9
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya bashe su ga waɗanda za su washe su. Ya sa magabtansu da suke kewaye da su suka sha ƙarfinsu, har ya zama Isra'ilawa ba su iya kāre kansu daga maƙiyansu ba.


Sai suka hana sarki Azariya, suka ce masa, “Ba aikinka ba ne, Azariya, ka ƙona turare ga Ubangiji, wannan aikin firistoci ne, 'ya'yan Haruna, waɗanda aka keɓe su don ƙona turare. Fita daga wurin nan mai tsarki, gama ka yi kuskure, ba za ka sami daraja daga wurin Ubangiji Allah ba.”


Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.


Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”


Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ