Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 4:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Ta zauna a gindin giginyar Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Isra'ilawa sukan haura zuwa wurinta don ta yi musu shari'a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Takan yi zaman shari’a a ƙarƙashin Dabinon Debora tsakanin Rama da Betel, a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuwa sukan zo wurinta don tă yi musu shari’a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 4:5
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga abin da Ubangiji ya ce, “An ji murya daga Rama, Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta, ba su.


Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.


Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa.


Suka yi ta yi wa jama'a duka shari'a kullayaumin, amma matsaloli masu wuya sukan kawo wa Musa, ƙananan kuwa sukan yanke da kansu.


Yanzu sai ka saurari maganata, zan ba ka shawara, Allah kuwa ya kasance tare da kai. Za ka wakilci jama'a a gaban Allah, ka kai matsalolinsu gare shi.


Kashegari da Musa ya zauna garin yi wa jama'ar shari'a, mutane suka kekkewaye shi tun dage safiya har zuwa yamma.


Can Debora, ungozomar Rifkatu ta rasu, aka kuwa binne ta a gangaren Betel, a ƙarƙashin itacen oak, don haka ana kiran wurin, Allon-bakut.


Sama'ila kuwa ya rasu. Dukan Isra'ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.


Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.


A sa'ad da suke da wata matsala sukan zo wurina, ni kuwa nakan daidaita tsakanin mutum da maƙwabcinsa, nakan kuma koya musu dokokin Allah da umarnansa.”


Debora, matar Lafidot, ita ce annabiya. Tana hukuncin Isra'ilawa.


Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da mashinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi.


Sa'an nan kuma ya koma gidansa a Rama inda kuma yakan yi wa Isra'ilawa shari'a. Ya kuma gina wa Ubangiji bagade a can Rama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ