Saboda haka zuriyarsu suka shiga, suka mallaki ƙasar Kan'ana. Ka rinjayi mutanen da suke zama a can. Ka ba jama'arka iko su yi yadda suke so Da mutane, da sarakunan ƙasar Kan'ana.
Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.
Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama'arsa.
Barak kuwa yana bin sawun Sisera. Da Yayel ta gan shi, sai ta fita, ta tarye shi, ta ce masa, “Ka zo, zan nuna maka inda mutumin da kake nema yake.” Ya shiga alfarwarta, sai ga Sisera nan kwance matacce da turke a gindin kunnensa.