Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 3:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Bayan Ehud kuma, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya kashe Filistiyawa ɗari shida da tsinken korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Bayan Ehud, sai Shamgar ɗan Anat, wanda ya karkashe Filistiyawa ɗari shida da sandar korar shanun noma, shi ma ya ceci Isra’ila.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 3:31
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A zamanin Shamgar ɗan Anat, a zamanin Yayel, Ayarori suka daina bi ta ƙasar, Matafiya suka bi ta ƙananan hanyoyi.


Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.


Da majajjawa da dutse kawai Dawuda ya ci nasara da Bafilisten. Ya buge shi, ya kashe shi ba tare da takobi a hannunsa ba.


Taron jama'ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da mashi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.”


Ya kuwa sami sabon muƙamuƙin jaki, ya ɗauka ya kashe mutum dubu da muƙamuƙin.


Sa'ad da Isra'ilawa suka zaɓi baƙin alloli, Sai ga yaƙi a ƙasar. Ba a ga garkuwa ko mashi A wurin mutum dubu arba'in na Isra'ila ba.


Sa'an nan Ubangiji ya naɗa musu mahukunta masu ƙarfi da suka cece su daga waɗanda suka washe su.


A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.


Sojojin Ammonawa kuwa, suka tattaru, suka kafa sansani a Gileyad. Isra'ilawa kuma suka tattaru, suka kafa nasu sansani a Mizfa.


Ubangiji kuwa ya husata da Isra'ilawa, ya ba da su ga Filistiyawa, da Ammonawa.


Bayan rasuwar Ehud, Isra'ilawa suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji.


A ranar nan Isra'ilawa suka rinjayi Mowabawa. Ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya har shekara tamanin.


Amma suka bar bin Ubangiji Allahnsu. Ubangiji kuwa ya bashe su a hannun Sisera, shugaban rundunar Yabin, Sarkin Hazor, da a hannun Filistiyawa, da kuma a hannun Sarkin Mowab, suka yāƙe su.


Ubangiji ya amsa musu, ya ce, “Ban cece ku daga hannun Masarawa, da Amoriyawa, da Ammonawa, da Filistiyawa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ