Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”
Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al'ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa'ad da al'ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al'umma tana da hikima da ganewa.’