Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 20:42 - Littafi Mai Tsarki

42 Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Saboda haka suka tsere a gaban Isra’ila zuwa wajen hamada, amma ba su iya tsere wa yaƙin ba. Mutanen Isra’ila da suka fito daga cikin birnin suka karkashe su a can.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 20:42
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila! Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba. Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?


Sun yi zurfi cikin rashin gaskiya Kamar a kwanakin Gibeya, Ubangiji zai tuna da muguntarsu. Zai hukunta su saboda zunubansu.


Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.


Sa'ad da Isra'ilawa suka gama karkashe mazaunan Ai duka a jeji inda suka fafare su, sai Isra'ilawa suka koma Ai, suka karkashe waɗanda suke cikinta.


Sai Joshuwa da mutanensa duka suka nuna kamar an rinjaye su, suka yi ta gudu, suka nufi jeji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ