Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.
Horarrun sojojin Isra'ila, su dubu goma (10,000), suka faɗa wa Gibeya. Yaƙi kuwa ya yi zafi, amma mutanen Biliyaminu ba su san masifa tana gab da su ba.
Za ka yi wa Ai da sarkinta kamar yadda ka yi wa Yariko da sarkinta, sai dai ganima da dabbobinta ne za ku washe domin kanku. Ku yi kwanto a bayan birnin.”