Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 20:27 - Littafi Mai Tsarki

27-28 Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?” Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Isra’ilawa suka nemi nufin Ubangiji (A kwanakin nan akwatin alkawarin Allah yana can,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 20:27
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da jama'ar Isra'ila suka ci ƙasar, sai suka tattaru a Shilo inda suka kafa alfarwa ta sujada.


Isra'ilawa suka tashi suka tafi Betel. A can suka yi tambaya ga Allah suka ce, “Wace kabila ce daga cikinmu za ta fara faɗa wa kabilar Biliyaminu?” Ubangiji ya ce, “Kabilar Yahuza ce za ta fara.”


“ ‘Ku tafi Shilo wurin da na fara zaunar da sunana, ku ga abin da na yi mata saboda muguntar mutanena Isra'ila.


Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.


Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”


Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”


Sa'ad da ka wuce nan, ka ci gaba zuwa itacen oak a Tabor, a nan mutum uku da suke haurawa zuwa ɗakin Allah a Betel za su gamu da kai. Ɗaya yana ɗauke da 'yan awaki uku, ɗaya kuma yana ɗauke da malmalar abinci guda uku, ɗayan kuwa yana ɗauke da salkar ruwan inabi.


Har wa yau ban taɓa zama a ɗaki ba, tun lokacin da na fito da Isra'ilawa daga Masar, amma a alfarwa nake kai da kawowa daga wannan wuri zuwa wancan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ