Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Mahukunta 20:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu goma sha takwas (18,000) daga cikin Isra'ilawa. Dukan waɗannan da aka hallaka horarru ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 A wannan lokaci, da mutanen Benyamin suka fito daga Gibeya don su yaƙe su, sai suka sāke kashe Isra’ilawa dubu goma sha takwas, dukansu ɗauke da takuba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Mahukunta 20:25
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Mutanen Biliyaminu kuwa suka fito daga birnin suka hallakar da mutum dubu ashirin da biyu (22,000), daga cikin mutanen Isra'ila a ranar.


Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!


In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.)


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


Gajimare da duhu sun kewaye shi. A kan adalci da gaskiya ya kafa mulkinsa.


Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”


Sai mutanen Isra'ila suka tafi su kara da mutanen Biliyaminu a rana ta biyu.


Dukan rundunan Isra'ilawa suka haura zuwa Betel, suka yi makoki, suka zauna a gaban Ubangiji suka yi azumi har maraice. Sa'an nan suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa da na salama.


“Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa, Da safe yakan cinye abin da ya kaso, Da maraice kuma yakan raba abin da ya kamo.”


Ubangiji ya ce, “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra'ila! Tun daga wancan lokaci kuka yi ta ci gaba. Ashe, yaƙi ba zai tarshe su a Gibeya ba?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ